A yammacin jiya a kayi bikin buɗe gasar ƙwallon kwando a jahar Kano gasar da aka yiwa laƙabi da Malikawa Basketball Championship kuma gasar itace karon farko.
Manyan baƙi sun hallaci bikin buɗe wannan gasa kuma gasar ta ƙayatar sosai da sosai inda wasanni biyu kawai aka fafata a yammacin na jiya Laraba.
Saidai kafin a fara fafata wasannin daga cikin masu ruwa da tsaki na wannan gasa wasu sunyi jawabin cewa akowacce shekara za a dinga saka wannan gasa ta ƙwallon kwando domin ci gaba da farfaɗo da harkar wasanni a jahar ta Kano musamman gasar ta ƙwallon kwando.
An fafata wasanni biyu a jiyan inda ƙungiyar ƙwallon kwando ta Paki Warriors tasha da kyar ahannun Bokavu Blinks daci 13 da 12. Itama Thunders tasha dakyar a hannun ƙungiyar ƙwallon kwando ta Ƙofar Mata daci 18 da 17.