Da sanyin safiyar nan ce dai ta Litinin, Yan bindiga su kayi awon gaba da Daliban Makarantar Bethel Baptist dake Maraban Rido na karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna.
Wani dalibi daya bukaci a sakaye sunan shi ya tabbatar da wa da Jaridar LEADERSHIP afkuwar lamarin, inda ya ce, yan’bindigan sun kutsa cikin makarantar ne da misalin karfe 2 na safen yau, inda suka fara harbi Kan me uwa da wabi kafin su dauki daliban.
A cewar shi anyi garkuwa da Dalibai da dama a makarantar, Amma wasu Dalibai hudu sun tsira daga harin, inda daga bisani suka dawo makarantar.
Wata majiya ta ce ” An harbi jami’an soji biyu, Amma bazan iya tabbatar da cewa sun mutu ba, ko suna Raye ba” inji majiyar
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba zanyi Murabus daga siyasa ba har sai na mutu– inji Ibarhim Shekarau
Majiyar ta Kuma cigaba da cewa, ” a bune Mai matukar wuya a iya kididdge yawan daliban da aka diba a yanzu haka” inji majiyar
Jaridar LEADERSHIP ta kuma ruwaito cewa, duk Yun kurin da ta yi, na ji tabakin Jami’in rundunar yan’sandan jihar Kaduna Mohammad Jalige ta wayar salula, domin ji ta bakinshi dangane da wanna lamari abun ya citira, har izuwa lokacin da ta hada wannan rahoto.
Akwai Karin bayani nan da anjima……..
Comments 1