Sarkin Bai Kano kuma Hakimin Dambatta, Alhaji Mukhtar Adnan, ya rasu ne a jiya Juma’a.
Majiyoyi na kusa da iyalan sun bayyana cewa Tsohon kwamishinan ilimi na farko a jihar Kano ya rasu ne da sanyin safiyar Juma’a bayan gajeriyar rashin lafiya yana da shekaru 95 a duniya.
Kamar yadda tarihi ya nuna, tsohon Sarkin Kano, Sir Muhammadu Sanusi I, ya nada Adnan a matsayin Sarkin Bai a shekarar 1954, ya gaji mahaifinsa.
Ya kuma kasance dan majalisar wakilai a lokacin jamhuriya ta daya kuma an nada shi kwamishinan ilimi na farko na jihar Kano a shekarar 1968.
Kafin rasuwarsa, Adnan ya kasance dan majalisar masarautar Kano mafi dadewa tun kafuwar masarautar a karni na 19. Ya yi aiki tare na tsawon shekaru 63 a matsayin hakimi, kansila da kuma sarki.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya ce mutuwar Sarkin Bai faduwa ce ta duniya Baki daya, Wanda Kuma ya kasance mai dimbin tarihi.
Shugaba Buhari ya ce marigayi Sarkin Bai Kano “babban mutum ne mai tarihi wanda ya yi fice a harkokin siyasa da al’adunmu.”
Sanarwar ta Garba Shehu ta kara da cewa “Tsarin Mukhtar Adnan na yin hidimar masarautar Kano na tsawon shekaru 63 kuma a matsayinsa na babban mai gabatar da kara a majalisar dokokin jamhuriya ta farko ya ba shi damar zama daya daga cikin manyan mutane a tarihi”
A cikin sakon ta’aziyya ga iyalan, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya bayyana rasuwarsa a matsayin “rasa wani abu mai wuyar gaske, mai matukar tarbiya kuma mai kishin kasa.”
Gwamnan ya ce a ko da yaushe jihar za ta yaba da irin gudunmawar da marigayi sarkin ya bayar wajen ganin an samu ci gaba a jihar.
“A matsayina na dan majalisar tarayya da ya yi aiki a majalisar dokokin kasar a jamhuriya ta farko, Dr Mukhtar Adnan yana daya daga cikin ’yan siyasar da suka tsara tsarin dimokuradiyyar mu zuwa halin da muke ciki na ci gaba da rayuwa a halin yanzu,” in ji Gwamna Ganduje.
An yi jana’izar marigayi Sarkin Bai Kano a gidansa da ke Dambatta bayan sallar jana’izar da babban limamin Dambatta Malam Nasir Abubakar ya jagoranta.