By Abbas Yakubu Yaura
An bukaci jami’an tsaron farin kaya na civil defence masu kula da Karamar Hukumar Gaya da suyi aiki tare da sarakunan Gargajiya don karfafa sha anin tsaro a yankin.
Maimartaba Sarkin Gaya Dr, Aliyu Ibrahim Abdulkadir ne yayi wannan kiran a lokacin da yake karbar bakunchin babban jami’i mai kula da karamar hukumar yayin daya kai masa ziyarar aiki a fadarsa.
Dakta Aliyu Ibrahim yakara dacewa yin aiki tare da masu rike da masarautun gargajiya ne za a kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro dake addabar yankunan masarautun Gargajiya dake fadin kasar nan.
Yakuma yaba musu bisa ziyarar da suka kai da kuma irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ganin an sami cikakken tsaro, tareda bada tabbacin cigaba da basu gudunmawa da hadin kan daya dace don cimma nasarar kawo karshen aiyukan bata gari a yankin.
Dayake nasa jawabin babban jami’in hukumar tsaro ta farin kaya mai lura da ofishin na masarautar ta Gaya, sufurintanda Mallam Ali Muhammad, cewa yayi sun ziyarci fadar Maimartaba Sarkin ne don su jaddada godiyar su bisa yadda masarautar ke basu gudunmawa wajen ganin aiyukansu na gudana yadda ya dace.
Mallam Ali Muhammad ya kuma kara da cewa hukumar tasu ta turo karin ma aikata mata da zasu yi aiki a cikin gidan mai martaba Sarkin kamar yadda masarautar ta nema.
A wani cigaban kuwa Masarautar Gaya ta nada sabbin limamai guda biyu wadanda aka naɗa sun haɗar da Imam Mallam Hassan Sunusi zai jagoranchi masallacin Tudun Mallam Mahdi dake garin dagacin Tsakuwa a Karamar Hukumar Dawakin Kudu sai Mallam Ahmad Tijjani Garba zai jagoranchi masallacin Amarawa dake karamar hukumar Warawa.
Dayake yi musu jawabi Maimartaba Sarkin Aliyu Ibrahim ya umarce su dasuyi amfani da ilimi su wajen kawo sauyi da ilimin tar da al ummar su, kuma su guji sanya siyasa acikin hudubarsu ko lokacin da suke gudanar da wa’azi, sannan su tabbata sun hada kan al’ummar da cigaba da neman sanin yadda zasu jagoranchi al’umma tareda cigaba da yiwa masarauta, jiha da kasa Addu’ar samun zaman lafiya.