Daga Sulaiman Musa
Shugaban rikon kwarya na Jam’iyyar APC a Jihar Gombe Mr. Nitte K. Amangal, ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan kagen da wasu gurbatattun mutane marassa kishin kasa ke ci gaba da kururutawa kan Ministan sadarwa da raya tattalin arzikin zamani Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami.
A wata sanarwa da Sabo Ibrahim
Sakataren yada labaran kwamitin rikon kwarya na Jam’iyyar APC a Jihar Gombe ya fitar a madadin jam’iyyar reshen Jihar Gombe, APC ta ce makiya kasar nan da ci gaban ta ne ke yayata wannan mummunan kage, tana mai kira ga Ministan da kar ya damu da kururuwar masu neman shafa masa kashin kaji.
Ta ce “Muna yabawa fadar shugaban kasa da masu fatan alheri kan yadda suka fito fili karara suka kare ministan daga wadannan zarge-zarge marasa tushe balle makama, wadanda kungiyoyi da daidaikun jama’a masu bakar aniya ga kasar nan ke yadawa.
“Muna tare da dan uwan mu Dr. Pantami, dan jam’iyya mai kishi da hazaka wadda ya yi fice a wannar jiha tamu ta Gombe. Don haka muna kira ga duk ‘ya’yan jam’iyyar mu suma su bi sahu su yi Allah wadai da wannan mummunan kage da aka yiwa Ministan don zaman lafiya da ci gaban kasar nan.
“Muna matukar alfahari da irin nasarorin da Dr. Pantami ke samu a majalisar zartaswa ta kasa, kuma wannan mummunan kage da ake yada wa a kan sa ba zai yi wani tasiri ba, hakan baya rasa nasaba da irin kyawawan manufofi da tsare-tsaren da yake aiwatarwa a sashin fasahar sadarwa da tattalin arzikin zamani don amfanin kasar da kyautatuwar tsaro da jin dadin al’ummar ta.”