Jam’iyyar APC a Jahar Kwara tace gangar jikin tsohon shugaban Majalisar Dokokin Jahar Ibrahim Isa Bio, Wanda ya bar Jami’iyyar zuwa PDP tana nan, duk da ya canja jam’iyyar.
Dayake magantawa akan canja sheƙar, Sakataren yaɗa labaru na Jam’iyyar APC na Jahar Tajudeen Aro yace “matakin da Bio ya ɗauka abune da yayi don raɗin kansa, kuma ko kaɗan ba yayi bane domin cigaban al’umma da kuma samun cigaba.
Jam’iyyar tace dukkanin al’ummar sa, da Dr Jamila Bio ɗiyar tsohon Ministan ta jini wanda a halin yanzu itace Babbar Mai Taimakawa Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq akan cimma muradun ƙarni suna tare da jam’iyyar APC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari baida maganin matsalolin Najeriya — Cewar Soyinka
“Ina tabbatar maku dacewar, ɗiyar tsohon Ministan da gaba ɗaya al’ummar Gure/Gwasoro tuni suka alwashin nuna amincewar su da APC gami da Ƙaramar Hukumar Baruten dama shiyyar Kwara ta Arewa, domin suna fuskantar mulkin gaskiya ta hanyar kawo cigaba da kuma wakiltar su a jaha dama ƙasa baki ɗaya,” inji Jam’iyyar.
Jam’iyyar tace an samu cigaba a ɓangaren samar da sabbin hanyoyi da Asibitoci, da gyara makarantu, musamman gina gidan rediyo na farko a jahar Kwara ta Arewa a Ƙaramar Hukumar Baruten.
Jam’iyyar tace “Duk da bama son rasa ko mutum ɗaya na jam’iyyar, Alhaji Bio Ibrahim nada damar da zai tsaya takarar Sanata a ƙarƙashin kowacce jam’iyyar daya ke ra’ayi.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar, tsohon Shugaban Majalisar Dokokin kuma Minista, a ranar Alhamis ya canja sheƙa daga Jam’iyyar APC zuwa PDP a mazaɓar sa ta Gure/Gwasoro ta Ƙaramar Hukumar Baruten ta Jahar.