Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta ce jam’iyyar APC ba ta da dan takarar Sanatan Yobe ta Arewa da Akwa Ibom Arewa maso Yamma.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, mai wakiltar Yobe ta Arewa na fafutukar samun tikitin jam’iyyar bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC. A gefe guda kuma, tsohon gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio shi ma yana fafatukar neman tikitin jam’iyya mai mulki ta tsayawa takarar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma. Akpabio ya kuma nemi takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.
Sai dai kwamishinan hukumar INEC na kasa, Festus Okoye ya ce hukumar zabe ba ta amince da duk wani dan takarar jam’iyyar APC na shiyyar sanatoci biyun ba.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/2023-ana-zargin-wani-%c9%97an-takarar-shugabancin-najeriya-da-%c9%97aukar-nauyin-%c6%b4an-taadda/
“A wadannan mazabu guda biyu an gabatar da sunaye guda biyu kuma hukumar ta yanke shawarar cewa sunayen ba mutanen da suka fito daga sahihin zaben fidda gwani na jam’iyyar ba ne kuma ba mu buga sunayensu ba.” Inji Okoye yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a shirin Sunday Politics.
Ya kara da cewa, “APC ce ta saka sunayen su (Lawan da Akpabio) zuwa cibiyar ‘yan takarar mu amma hukumar ta yanke shawarar cewa ba su ne ‘yan takarar da suka fito daga sahihin zaben fidda gwani na jam’iyyar ba.
“Hukumar ba ta buga sunayensu da bayanansu a mazabarsu ba. Don haka abin da ake nufi shi ne, har yau jam’iyyar APC ba ta da ‘yan takara a wadannan mazabu biyu.”
A makon da ya gabata ne INEC ta ki amincewa da takardar shaidar kammala aikin tantance Lawan da Akpabio a matsayin ‘yan takarar sanata a zaben 2023.
“Hukumar bata buga fom din mutanen biyu da ake magana a kai ba,” in ji INEC.
“Shawarar da Hukumar ta yanke ya jawo matakin shari’a wanda har yanzu ake ci gaba da gudanar da ita.
“Saboda haka, ya saba wa hankali da tinani, tare da gabatar da takaddun likita da ake zargin sun amince da su a matsayin ‘yan takara lokacin da lamarin ya kasance a fili.”
CHANNELS TV