Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar yace Jam’iyyar APC bata ƙarfin haɗa kan Ƙasar, yana mai cewa rashin iya Mulkin APC ya rarraba kawunan Ƴan Ƙasar.
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa yayi wannan jawabin a Minna a ranar Alhamis a lokacin da yayi taro da Dalaget na Jam’iyyar PDP domin neman goyon bayan su a zaɓen Fidda Gwani mai zuwa.
Yace Jam’iyyar APC bata da ƙarfin fito da Najeriya daga halin da take ciki ba, kuma bata iya bada aikin yi ga Mata da Matasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ina Goyon Bayan Tinubu Dari Bisa Dari— Gwamna El-Rufa’i
“Ina roƙo a gare ku da kada ku zaɓi APC a Babban Zaɓe, basu da ƙarfin ƙwarewar haɗa kan Ƙasar, kuma basu iya bada wani Tallafi ga Mata da Matasa.”
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasar ya ƙara dacewa, an bar Jam’iyyar PDP ba tare da wani zaɓi ba, illa ta ƙwace Mulki daga APC domin gyara kura-kuren da Jam’iyyar mai Mulki ta aikata.
Atiku yayi kira ga Mambobin Jam’iyyar dasu zama Tsintsiya maɗaurin ki ɗaya, yana mai cewa hakan ne zai tabbatar da samun nasarar cin kujerar Gwamna a zaɓen Shekarar 2023.