APC ce ta biyani maƙudan kuɗaɗe domin in goyi bayan Tinubu — Mawaƙi Portable
Mawaƙi Mai tasowa a Najeriya Habeeb Okikiola da akafi sani da Portable ya bayyana cewar Jam’iyyar APC ta biya shi kuɗaɗe domin ya goyi bayan Bola Ahmed Tinubu a Babban Zaɓen Shekarar 2023.
A ranar Laraba, Mawaƙin ya tura wani bidiyo a shafin sa na Instagram tare da Gwamnan Jahar Osun Gboyega Oyetola. A cikin bidiyon ya nuna goyon bayan sa ga Ɗan Siyasar Gwamna da za’a gudanar a ranar 16 ga watan Julin Shekarar 2023 a Jahar Osun.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar FRSC Ta Yabawa IGP Kan Haramta Amfani Da Lambobin SPY A Fadin Kasar
A wani bidiyon, Mawakin ya nuna wasu kuɗaɗe bayan taron sa da Gwamnan. Daga bidiyon, an ɗora kuɗaɗen a takarda dake da wata alamar Jahar Osun akan ta.
Ƴan Najeriya da suka maida jawabi akan bidiyon sun bayyana fushin su ga Portable da Gwamnan. Sun kira sunan Gboyega Oyetola, suna ƙalubalantar sa da amfani da kudin haraji domin ya ci zaɓe.
A wani sabon bidiyo daya fitar, ya bayyana cewa APC ta biya shi kuɗaɗe domin ta goyi bayan Ɗan Takarar su, kuma a shirye ya nema wa Jam’iyyar goyon baya tunda an biya shi.
Portable yace an taɓa biyan sa kuɗaɗe ya zagi Bola Ahmed Tinubu a shekarun baya wanda yayi, yace masu zaginsa, su barshi yayi aikin sa.
Amma Uwar Jam’iyyar APC ta Ƙaryata batun biyan kuɗaɗen ga Mawakin domin ya goyi bayan su