• Gwamna jihar Kano Ganduje ya ce, APC ce wurin Gwaje-Gwaje a Dimokuradiyyar Yan Nigeria.
• Ganduje ya bayyana hakan ne a wurin taron kaddamar da kwamitin da zai wayar da kan Al’uma, game da rajistan masu zabe ta hanyar yanar gizo.
• Dukkannin wadanda suka yi jawabi a wurin taron, sun jaddada aniyar su, na cigaba da bin dukkannin umarnin gwamnan Ganduje.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana jam’iyar APC Mai Mulki amastayin wurin kwaje-kwaje a Dimokuradiyyar Nigeria, inda ya tabbatar da cewa, ba Abu ne maiyuwu ba, a iya kada jam’iyar.
Ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi, a wurin taron kaddamar da kwamitin jam’iyar APC, da zai wayar da kan al’uma, kan Shirin hukumar zabe ta kasa INEC, na rajistan masu zabe ta yanar gizo, da ya gudana a dakin taro na Africa House, dake fadar gwamnatin jihar a garin Kano.
A cewar shi“Jam’iyar APC ce wurin Gwaje-Gwaje a Dimokuradiyyar Nijeriya, wuri ne da mu keyin abubuwa a kimiyance, kuma komai kaga mun yi a wannan jam’iyar, sai da muka lissafa shi tukunnan” inji shi.
“Mun yarda da curewa wuri guda a dukkanin abun da mu keyi, Kuma kunsan nan ne wurin Gwaje-gwaje, inda zaka yi amfani da kimiyya don tunkarar kasuwancin ka” a cewar Gwamnan.
KARANTA WANNAN LABARIN: An kama su kayi garkuwa da Mahaifin Gwamnan jihar Filato
Taron ya sami halartan jagororin jam’iyar APC, wanda su ka hadar da, Mataimakin Gwamnan jihar, Shugaban majalissar dokokin jihar, Sakataran gwamnatin jihar, Kwamishinoni da wasu manyan jami’ai na majalissar zartarwar jihar, gami da Ciyamomin kananan hukumomin, da kuma wasu masu ruwa da tsaki a Jam’iyar ta APC reshen jihar Kano.
Kazalika dukkannin wadanda su kayi jawabi a wurin taron, sun jadda aniyar su, na bin dukkannin umarnin gwamnan Gamduje, domin daga martaba jihar Kano da kuma cigaban ta.
Inda kuma suka, yaba wa Gwamna Abdullahi Ganduje, bisa kokarin da ya ke yi na hadakan jagororin jam’iyar baki daya.