APC ce Zata lashe Zaɓen Gwamnan Osun — Inji Buhari
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yace yana tabbacin cewa Jam’iyyar APC Mai Mulki itace zata cinye zaɓen Gwamnan Jahar Osun mai zuwa.
Shugaban ya bayyana haka a ranar Laraba a lokacin da yayi bikin bada tuta ga Ɗan Takarar Gwamna Adegboyega Oyetola.
KARANTA WANNAN LABARIN: Babbar Sallah: Yan sanda Sun Kama Mutum 2 Bisa Zargin Satar Ragon Layya A Ogun
Buhari, ya bada tabbacin cewa Jam’iyyar a shirye take ta cigaba da kawo cigaba a Jahar, yana mai yabawa Gwamna Oyetola da irin aikin da yayi a wa’adin mulkin sa na farko.
Shugaban Ƙasar ya kuma yabawa Shugaban Gangamin Yaƙin Neman Zaɓe na Jahar Osun, mai Gwamna Babajide Sanwa-Olu da Dr Abdullahi Umar Ganduje, da Gwamnan Jahar Neja Abubakar Sani Bello, da irin jajircewar su waje yin gangami domin sake zaɓen Gwamna Oyetola.
“Ina yi maku fatan Alkhairi” Garba Shehu ya naƙalto Shugaban Ƙasar na bayyana wa.
A maida martanin sa akan gayyatar da akayi mashi na halartar gangamin yaƙin neman zaɓe na ƙarshe, a sati mai zuwa, ya ce “zanje wurin domin in ƙarfafa maku gwuiwa.”
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa Sanata Abba Kyari wanda ya gabatar da Ɗan Takarar a madadin Sanata Abdullahi Adamu, Shugaban Jam’iyyar, ya yabawa Shugaban daya Jagoranci Jam’iyyar domin samun nasara.
Ya bayyana Oyeto a matsayin Gwamna daya yi ayyuka masu yawa a Wa’adin sa na farko, kuma cancanta a zaɓe shi na biyu.
Ya kuma bayyana fatan cewa Jam’iyyar zata samu nasara a Babban Zaɓen Shekarar mai zuwa na watan Fabrairu.