Daga Sulaiman Musa
Jami’iyyar APC reshen jihar Bayelsa ta bayyana aniyarta na yin kiranye ga mambar majalisar dokoki mai wakiltar mazabar Brass Constituency 1, Daniel Charles, bisa sauya shekarsa zuwa jam’iyyar PDP.
APC ta bakin shugabanta a karamar hukumar Brass, Baribote Solomon, ta misalta sauya shekan dan majalisar a matsayin son zuciya na kashin kai ba don al’umma ba.
Ya bayyana cewar don haka jam’iyyar za ta fara shirye-shiryen yin kiranye ga Charles saboda tikitin da ya ci kujerar da shi nata ne.
Solomon ya bayyana cewar jam’iyyar APC a jihar Bayelsa a dinke take a matsayin tsintsiya madaurinki daya.