Jam’iyyar APC reshen jihar Osun, ta bukaci da a gaggauta can zawa kwamishinan ‘yan sanda, Patrick Kehinde Longe wurin aiki.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a ranar Laraba a Osogbo.
KARANTA WANNAN LABARIN: A Na Tsaka Da Rashin Kuɗi; Buhari Zai Shilla Ƙasar Habasha
Sannan APC ta zargi jam’iyyar PDP da daukar nauyin ‘yan daba a jihar.
Tajudeen Lawal, Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Osun, wanda Daraktan Yada Labarai na Jam’iyyar Kola Olabisi ya wakilta, ya bayyana cewa mambobinsu ba su san zaman lafiya ba tun bayan da kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Jihar Osun ta yanke hukuncin da bai yi wa PDP Osun da Gwamna Ademola Adeleke da di ba.
“Da a ce ‘yan barandan da Adeleke ke daukar nauyinsu ba su yi kisa ba, ko nakasasu ko kuma su kai hari ga mambobinmu a garuruwa da kauyukan Jihar, masu rike da mukaman jam’iyyar PDP za su rika shirya zanga-zangar da ta dauki nauyin shiryawa a cikin Jihar da kuma wajenta, har ya zuwa Abuja domin a yi karyar cewa korarren gwamnansu da kotun ta tabbatar da jabun takardun makaranta a kansa, waliyyi ne.
“Ya zama aikin da ya wuce na matasa da tsofaffi a bangaren PDP na Jihar Osun, masu biyayya ga Daular Siyasa ta Ede, su rika tozarta bangaren shari’a ta hanyar kiran ‘ya’yan kotunan Gwamna da sunayen da ba a buga ba tare da zarge-zargen da ba su da tushe balle makama. su, ba inda za mu dosa ba ne, kasancewar rikicin yana tsakanin PDP da bangaren shari’a,” inji shi.
Lawal ya yi nuni da cewa yawancin mambobinsu da ke karamar hukumar Atakunmosa ta Gabas da ke jihar an yi watsi da su daga garin, kuma wasu da ake zargin ‘yan PDP ne suka lalata musu dukiyoyinsu da gangan a matsayin wani shiri na hana su shiga zaben da ke tafe.
“Yanzu haka wasu daga cikin mambobinmu suna yin hijira suna tsugunne a garuruwan Ilesa, Ile-Ife, Osogbo da sauran garuruwa don gujewa kai hare-haren siyasa,” in ji shi.
Lawal ya bayar da misali da harin da aka kai ranar 2 ga watan Fabrairu, 2023 a karamar hukumar Irewole inda aka kashe Saheed Oyegunju.
Jam’iyyar ta bayyana cewa tana dauke da bayanai da ke bayyana shirye-shiryen da aka yi tsakanin jam’iyyar PDP a jihar da ‘yan sanda na cafke wasu shugabannin ta.
Da yake mayar da martani, Akindele Adekunle, shugaban riko na PDP na Osun ya bayyana cewa CP Longe bai yi wa PDP son rai ba kamar yadda APC ta yi ikirari.
Da yake karyata rade-radin cewa ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne suka kai wa ‘yan APC hari, ya kara da cewa ‘yan APC ne ke kai wa ‘yan PDP hari a jihar.
A halin da ake ciki, CP Longe a nasa bangaren ya bayyana cewa yana gudanar da ayyukansa cikin kwarewa kuma ana gudanar da bincike kan lamarin hare-haren da jam’iyyun siyasa suka kai.
Da yake magana ta bakin mai magana da yawun rundunar, Yemisi Opalola, Longe ya bada tabbacin cewa za a binciki duk wasu kararraki tare da gurfanar da masu laifin.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: NECO Ta Fitar Da Sakamakon Jarabawar SSCE ta 2022
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa NECO, ta sanar da fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Nuwamba/Disambar shekarar 2022, SSCE.
Magatakardar NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Minna, jihar Neja, ya ce mutane 59,124 ne suka zana jarrabawar, maza 31,316, wanda ke wakiltar kashi 52.96, yayin da dubu 27,808, wanda ke wakiltar kashi 47.03 cikin 100 mata ne.