- Jam’iyyar APC reshen jihar Kogi ta dakatar da dukkan jami’an zartaswa na daukacin sassan karamar hukumar Igalamela/Odolu.
- Jam’iyyar ta kuma zargi jami’an da aka dakatar da karkatar da kudaden jam’iyyar da nufin durkusar da ita a jihar.
- APC tace nan take an kafa wani kwamitin rikon kwarya don gudanar da al’amuran jam’iyyar a kananan hukumomin da abin ya shafa.
Jam’iyyar All Progressives Congress APC reshen jihar Kogi ta dakatar da dukkan jami’an zartaswa na daukacin sassan karamar hukumar Igalamela/Odolu da ke jihar bisa zargin cin amanar jam’iyyar.
Jam’iyyar ta kuma zargi jami’an da aka dakatar da zargin karkatar da kudaden jam’iyyar da nufin durkusar da jam’iyyar a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ganduje Ya Mayar Da Martani Kan Sautin Hirar Su Dake Yawo A Kafofin Sada Zumunta
Wata sanarwa da sakataren jam’iyyar APC na jihar, Joshua Onoja ya fitar a Lokoja a ranar Lahadi, ya ce jam’iyyar na binciken jami’an da aka dakatar.
Onoja ya bayyana cewa dakatarwar da kuma rusa su ya biyo bayan rahotanni masu tayar da hankali da ake zargin shugabannin mazabun da na kananan hukumomi na jam’iyyar sun saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Ya bayyana hakan a matsayin abin takaici da damuwa yadda aka samu wadannan jami’an wadanda a ka’ida sune zasu kasance masu kula da tsaftar kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
“An kafa zarge-zargen cin amanar jam’iyyar da kuma karkatar da kudi don raunana jam’iyyar a kan wadannan shugabannin jam’iyyar a yanzu da ake gudanar da bincike mai zurfi akan su.
“Wannan ne ya sa daukacin shugabannin jam’iyyar na karamar hukumar Igalamela/Odolu aka rushe su tun daga mazabu har zuwa kananan hukumomi.
Sakataren ya bayyana cewa nan take za a kafa wani kwamitin rikon kwarya don gudanar da al’amuran jam’iyyar a kananan hukumomin da abin ya shafa har sai an kammala cikakken rahoton kwamitin binciken.
Ya umurci jami’an da aka dakatar da su mika dukkan kayayyakin jam’iyyar da ke hannunsu ga sakatariyar jihar da ke Lokoja.
Kazalika ya gargadi jami’an da aka kora da su daina bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar.
Da yake mayar da martani, daya daga cikin jami’an da aka dakatar, wanda ya bukaci a sakaya sunan sa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN cewa, “muna bin umarnin dakatarwar da shugabannin jam’iyyar mu na jihar mu suka yi mana.
NAN
A wani labarin kuma, Duk Gwamnonin Najeriya El-Rufai Ne Ya Ciri Tuta Wajen Fadin Gaskiya Ba Tsaro – Inji Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike
Gwamna Nasir El-Rufa’i na Jihar Kaduna ya ce zai ci gaba da korar ma’aikata, tare da rusa gidaje wadanda aka gina ba bisa ka’ida ba.
Gwamna El-Rufai ya ce zai ci gaba da aikin rushe rushen har zuwa karfe sha daya na daren ranar 29 ga watan Mayu.