By Abbas Yakubu Yaura
Kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC dake mazabar Lembi a karamar hukumar Akko ta jihar Gombe, ya dakatar da tsohon dan majalisar wakilai.
Umaru Barambu ya wakilci mazabar Akko ta tarayya a lokacin da ya lashe zaben dan majalisar tarayya na shekarar 2015 da aka gudanar amma dan takarar jam’iyyar PDP Samaila Mu’azu Hassan ya kalubalanci samun nasararsa a gaban kotun.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Karamar kotun ta yi watsi da karar saboda rashin cancanta, Dan takarar na PDP ya garzaya zuwa kotun daukaka kara wanda ta bada umarnin sake gudanar da zabe.sai dai ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a ranar 25 ga watan Nuwambar shekarar 2015 ba tare da hamayya ba da kuri’u 318 na wakilai.
Da yake bayyana hakan a ranar Litinin, shugaban jam’iyyar na gundumar mazabar Gwani Audu, a sakatariyar jam’iyyar APC ta jihar, ya yi zargin cewa tsohon dan majalisar ya nuna alamun adawa da jam’iyyar, yana mai jaddada cewa shugabannin jam’iyyar ba za su amince da hakan ba.
Audu ya ce kwamitin zartarwa na mazaba ba zai bari kowa ya yi wa jam’iyyar zagon kasa ba musamman ganin zaben 2023 ya gabato don haka suka yanke shawarar dakatar da jiga-jigan jam’iyyar.
Sannan yace, “Ba ma son abubuwan da suka saba wa jam’iyya, saboda mun yi alkawarin yin biyayya ga jam’iyyar ba tare da bata lokaci ba. Ba ma son duk wani abu da zai karya jam’iyyar, Shi ya sa muka dakatar da shi har sai ya kai gare mu ya gyara.
“APC tana da karfi a gundumar mazabar Lembi, saboda haka ba ma son rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar, Don haka ba za mu lamunci duk wadannan ayyukan da suka saba wa jam’iyya ba. Muna goyon bayan gwamna gaba daya”.