Jam’iyyar APC mai mulki ta fara sayar da fom din tsayawa takara a zaben gwamnonin Bayelsa, Kogi da kuma Imo da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wakilin Majiyar Dimokuradiyya ya ruwaito cewa tuni masu neman takara suka fara karbar fom dinsu a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da ke Abuja kan kudi Naira miliyan 50.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Yuwuwar Tuchel Ya Koma Tsohuwar Kungiyarsa
Wani tsohon zababben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon, wanda ya samu damar amsan fom dinsa a ranar Juma’a, ya bukaci kwamitin zartaswar jam’iyar na kasa (NWC) da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar su zabe shi a matsayin dan takarar da aka amince da shi a zaben jihar.
Kotun koli ta kori Lyon na jam’iyyar APC a matsayin zababben gwamnan jihar Bayelsa a shekarar 2020, sa’o’i 24 kacal da rantsar da shi, saboda mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremienyo, ya gabatar da bayanan karya ga hukumar zabe ta kasa (INEC). domin nuna cancantarsa a zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.
A wata hira da manema labarai jim kadan bayan karbar fom dinsa, Lyon wanda lauyan Marlin Danier ya wakilta, ya ce tsayar da shi a matsayin dan takarar zai tabbatar da nasara ga jam’iyyar APC a zaben.
Danier wanda ya yi magana a madadin Lyon ya ce, “Shi ne kadai zai iya lashe zaben jam’iyyar APC a jihar Bayelsa. An gwada Cif David Lyon, an gwada shi kuma an amince da shi.
Hakazalika, shugaban ma’aikatan gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, Abdulkareem Asuku, shi ma ya samu sayin fom dinsa na tsayawa takarar gwamnan Kogi. Ya bayyana kwarin gwiwar cewa zai lashe zaben.
A wani labari kuma, Karancin Kudi: Buhari Ya Yi Amfani Da Gurguwar Shawara, Bayan Umarnin Kotun Koli — Keyamo
Mai magana da yawun kwamitun yakin neman zaben jam’iyyar APC-PCC, Festus Keyamo ya ce yana adawa da matsayar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan sabbin takardun kudin Naira. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Buhari ya amince da matakin da babban bankin Najeriya ya dauka na sauya tsofaffin kidin amma ya amince da sake rarraba tsohuwar N200.