Jam’iyyar APC ta gargadi shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu kan zargin karya da yake mata.
Felix Morka, Sakataren Yada Labarai na Kasa, ne ya fitar da sanarwar gargadin a ranar Talata.
Ayu, wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ne, kuma Minista, ya musanta cewa Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ba cika namiji ba.
KARANTA ANAN: Najeriya Da Poland Sun Sanya Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Fahimtar Juna
APC ta ce Ayu ya yi zargin cewa sauran miyagu na jam’iyyar ne suke dasa irin wadannan labaran a kafafen yada labarai da kuma haddasa rashin jituwa tsakaninsa da Wike.
Ayu, a cewar Morka, yana zufafawa ne akan abubuwan da basu kamata ba, kuma yana yin katsalandan don neman wasu mutane da zasu bashi kariya ta musamman da yake tunani.
Kakakin ya kara da cewa, da irin wannan tunanin na kubuta, ba abu ne mai wahala a ga dalilin da ya sa rugujewar jam’iyyar PDP ta yi kasa a gwiwa ba a idon sa.
A wani labarin kuma: Yajin Aikin ASUU: Ministan Ilimi Ya Shiga Ganawar Gaggawa Da Shugabannin Jami’o’i
Ministan ilimi, Adamu Adamu, tare da masu ruwa da tsaki irin su magatakardar hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sikandire, Farfesa Ishaq Oloyede; Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa, Farfesa Abubakar Rasheed; Emeritus Peter Okebukola da Nimi-Briggs; tare da dukkan shugabannin jami’o’in tarayya da masu goyon bayan shugabannin jami’o’in tarayya sun fara wani zama na musamman.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa zaman ya kasance na sirri ne, kuma zai mayar da hankali kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in take yi yanzu haka.