Kwamitin Ɗaukaka Ƙara da Jam’iyyar APC ta kafa ya bayyana cewa duk wani mamba nata dake da wani ƙorafi daya inganta akan zaɓen mazaɓu da tayi satin daya gabata a Jahar Zamfara, daya gabatar da ƙorafin shi.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Kwamitin Jam’iyyar Barista Mohammed Elegu ya sanyawa hannu da aka fitar a Gusau, Babban birnin Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojoji Sun Shiga Aikin Ceto Bayan Afkuwar Ambaliyar Ruwa A Birnin Vancouver Na Kasar Kanada
A cewar sanarwar, kwamitin a shirye yake ya duba duk wani ƙorafi da aka gabatar akan zaɓen Mazaɓu da aka gudanar a Jahar.
Ya umarci ƴaƴan Jami’iyyar masu ƙorafi dasu bada ƙorafin su a Sakatariyar Jam’iyyar dake kan hanyar Sokoto zuwa Zaria a Gusau Babban birnin Jahar.
Kwamitin ya buƙaci mambobin su dasu zama masu biyayya domin ciyar da Jam’iyyar a matakin gaba a Jahar.