inec

APC Ta Lashe Kananan Hukumomi 10 A Zaben Gwamna A Kogi

Rahotannin dake shigo mana a cikin daren nan na nuni da cewa; a zaben gwamna da aka yi a jiya Asabar a jihar Kogi, jam’iyyar APC na da kuri’a 369, 481 yayin da PDP ke da kuri’a 154, 179, sai jam’iyyar SDP na da kuri’a 8, 318.

APC ta lashe kananan hukumomi goma wanda ya hada da Adavi, Okene, Ogori/Magongo, Ijumu, da Kabba/Bunu, Ajaokuta, Kogi, Mopa-Muro, Okehi, Olamaboro. A yayin da PDP ta lashe kananan hukumomi takwas wanda suka hada da; Igalamela-Odolu, Omala, Yagba East, Yagba West, Ofu, Dekina, Ankpa, Bassa,  su kuma SDP ba su da ko karamar hukuma daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *