Apc

APC Ta Lashe Kujerar Majalisar Tarayya A Jihar Kuros Ribas A Zaben Maye Gurbi

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta ayyana Alex Egbonna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar dan majalisa mai wakiltan Mazabun Yakurr/Abi na Kuros Ribas a Majalisat Wakilai.

Malamin zaben, Alalibo Johnson, ne ya fadi haka ranar Lahadi a wurin tattara sakamakon zabe dake Ugep.

Alalibo, ya ce dan takarar jam’iyyar APC ya yi nasara ne da kuri’u 29,716 inda ya doke John Lebo na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 26,039.

Hukumar zaben ha ila yau ta bayyana Davies Etta na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe kujerar mai wakilta Mazabar Abi a Majalisar Jiha.

Dan takarar na PDP ya doke abokin hamayyarsa da kuri’u 13, 349, inda shi kuma ya tashi da kuri’u 8,792.

Sai dai INEC ta dakatar da za zaben da aka yi a rumfuna takwas dake gundumar Afafanyi/Igonigoni sakamakon rikcin da ya barke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *