Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC a zaben 2019, Obadiah Mailafia, ya bayyana yadda APC ta nemi ya dawo cikin tafiyar jam’iyyar saboda a yafe masa zunubansa. A Ranar Talata, 17 ga Watan Satumban 2019, Obadiah Mailafia ya ce jam’iyyar APC mai mulki ta yi kokarin janyo sa a jikin ta da nufin za a yafe masa laifin da bai taba aikatawa a duniya ba.
A cewarsa, Jiga-jigan APC sun yi tunanin ya na harin shigowa jam’iyyar ne bayan zabe. Mailafia ya yi wannan bayani ne lokacin da ya gana da manema labarai a Hedikwatar ADC a Garin Abuja. Obadiah Mailafia wanda ya taba rike kujerar mataimakin gwamnan babban bankin CBN ya ce: “Gabanin zabe, an matsa mani lamba, inda aka rika mani tambayoyi game da abubuwan da su ka faru a CBN kusan shekaru goma da su ka wuce, abubuwan da ba a sashe na ma su ka faru ba.”
Ya kara da cewa an nemi a kitsa mishi sharri da cewa idan na shiga APC, za a yafe mani. Na fada masu cewa me yasa su ba za su dawo jam’iyya ta ba? Ya ci gaba da cewa; har na tambaye su me zai hana Buhari dawowa ADC?” “Me ya ke da shi da ba ni da wanda ya fi sa? Na ce mutanen su ‘yan zamanin da ne za su ceci Nijeriya? Mutumin da bai taba amfani da kyamfuta ba. Me za su kara iya yi wa Nijeriya?” ya tambaya.
A game da shari’ar P & ID, tsohon ‘dan takarar ya ja-kunnen gwamnati da ta bi sannu a hankali ka da ta jefa kasar cikin babban rikici inda ya ce manyan duniya ne su ka kitsawa kasar kutungwila.