Kimanin mambobin jam’iyyar APC 2000 ne a karamar hukumar Dass ta jihar Bauchi suka fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
A lokacin da yake karbar wadanda suka sauya sheka a ofishin jam’iyyar PDP na Bundilin Dutse da ke gundumar Bundot, shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Dass, Alhaji Shatima Sani Korau, ya yaba musu bisa shigarsu jam’iyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyar PDP Ba Za Ta Sake Dawo Kan Karagar Mulki Ba– Tinubu
Korau, wanda ya bayyana jam’iyyar PDP a matsayin jam’iyyar siyasa daya tilo da ke da karfi a nahiyar Afirka, ya kuma umarce su da su marawa jam’iyyar baya domin ta ci gaba da rike matsayinta domin ci gaban kananan hukumomi, jiha, da kasa baki daya.
Ya kuma ba da tabbacin cewa majalisarsa a shirye take ta gudanar da mulkinta tare da kowa, ba tare da la’akari da wani bambanci ba.
Ya kuma kara da cewa, An ba su katin zama mambobin jam’iyyar PDP ne domin ba su damar shiga cikin harkokin jam’iyyar.
Shima da yake jawabi, Hon. Ibrahim Usman Dankade, babban mai binciken jam’iyyar PDP na shiyyar arewa maso gabas, ya bayyana taron a matsayin wata babbar dama ga jam’iyyar domin fuskantar kalubalen dake tafe a nan gaba.
Ya bukaci al’ummar Dass da su ci gaba da marawa kokarin jam’iyyar PDP baya.
A sakon sa na fatan alheri, mataimakin shugaban karamar hukumar Dass Hon. Ambasada Prince Nuhu (Wadata) Danmalikin Bundot, ya bayyana matakin a matsayin wata babbar alama da ke nuna nasarar jam’iyyar gabanin 2023.
Yayin da yake taya wadanda suka sauya sheka murnar daukar matakin da ya dace, Nuhu ya ce jam’iyyar PDP ita ce kawai kwarin gwuiwar ‘yan Najeriya.
A WANI LABARIN KUMA: Zulum Fitila Ne Abar Haskawa, Inji Gwamnan Jam’iyyar PDP
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana cewa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya kasance fitila ne abar haskawa ko bege a Najeriya da dabarun jagoranci.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Mohammed, wani gwamna ne a jam’iyyar PDP ne ya bayyana hakan a Bauchi ranar Lahadin nan, a lokacin da Zulum ya kai masa ziyarar ta’aziyyar rasuwar babban yayansa, Mista Bappa Mohammed