By Abbas Yakubu Yaura
Kimanin mambobin jam’iyyar (APC) a karamar hukumar Funakaye 11,000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP
Sai dai APC ta yi musu ba’a, inda ta ce sun sauya sheka ne saboda suna ganin ba za su iya samun tikitin takara a babban zaben shekarar 2023 ba.
Da yake jawabi a ranar Asabar yayin liyafar, wani jigo a jam’iyyar PDP, Abubakar Abubakar, ya tabbatar musu da cewa matsalolin da suka fuskanta a APC ba za su faru a sabuwar jam’iyyarsu ba.
Abubakar, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne daga shekarar 2007 zuwa 2011, ya bayyana cewa wadanda suka sauya sheka sun koma jam’iyyar PDP ne saboda rashin kulawar da jam’iyyar APC ta yi musu bayan sun yi kokarin ganin ta samu nasara a zaben shekarar 2019.
A cewarsa, “Na kasance dan jam’iyyar APC mai dauke da kati amma na rabu da ita saboda rashin tsari da rashin gudanar da aikin gwamnan jihar Muhammadu Inuwa Yahaya.
Abubakar ya kuma yi zargin cewa gwamnan bai yi amfani da ‘yan siyasar da suka taimaka masa wajen samun nasarar sa ba.
Da yake mayar da martani kan sauya shekar, jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar APC na Gombe, Moses Kyari, ya ce masu sauya shekar sun fice daga jam’iyyar ne saboda wasu dalilai na kashin kansu.
“Suna tunanin ba za su iya samun tikitin takara a zaben shekarar 2023 ba, don haka suka zabi komawa PDP,” in ji shi.