APC za ta lashe zaben 2023 tare da goyon bayan matasa – Buratai
Tsohon shugaban hafsan sojin kasa (COAS), Tukur Buratai, ya ce jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ita ce jam’iyyar da za ta lashe zabe a 2023.
Janar mai ritaya ya bayyana cewa jam’iyyar APC na da dukkan abin da ake da buƙata domin ganin ta ci zabe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nada Ni A Matsayin Ko-odinetan Matasa Na Yakin Neman Zaben Tinubu Abin Mamaki Ne – Yahaya Bello
Buratai ya yi wannan tsokaci ne a wajen taron shugabannin matasa da aka yi a Abuja ranar Litinin.
Ya bukaci matasa da su karfafa masu kada kuri’a su marawa jam’iyyar APC baya domin samun makomarsu da kuma bunkasa ci gaban Najeriya.
“Dole ne ku tattara masu zabe don ganin sun fito gaba daya domin zaben wanda ya dace.
“Na yi imani kun san wanda nake nufi. Jam’iyyar APC da goyon bayan matasa ita ce jam’iyyar da za ta yi nasara,” NAN ta ruwaito.
Buratai ya kuma shawarci matasa ‘yan kasa da su tashi tsaye wajen ci gaban kasar nan.
Tsohon hafsan hafsoshin sojin sama, Marshal Abubakar Sadique ya ce matasa ba za su iya cin gajiyar kujerar ba kafin 2023.
A wani labarin kuma: An gano matattun Dabbobi a Mahautar Kano
Hukumar kula da Kayayyakin da ake ci ta Jihar Kano (KSCPC) ta gano matattun dabbobi a Abattoir na Unguwa Uku Yan Awaki da ke karamar hukumar Tarauni.
Mukaddashin Manajin Darakta, Baffa Babba-Dan’agundi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kakakin sa, Musbahu Yakasai ya fitar.
An mika wa Hukumar bayanan game da dabbobin da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Litinin.