Jam’iyyar adawa ta APGA a ƙasarnan ta shawarci gwamnatin tarayya da ta guji amfani da karfin tuwo kan yan adawa.
A madadin haka jam’iyyar ta shawarci gwamnatin da ta yi amfani da hanyar lalama wajen shawo kan lamaran da suka sha karfinta.
Sakataren watsa labaran jam’iyar Barista Tex Okechukwu shine ya mika wannan shawara a yau Lahadi a birnin tarayya Abuja cikin ci gaba da shagulgular cika shekara shida na shugabancin Dakta Victor Ike Oye.
A cewar ya kamata gwamnati ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta shawo kan al’umma guri guda don gudun kawo rabuwar kanu tsakanin yan kasa.