A rana mai kama ta yau wato 6 ga watan Satumba na shekarar 1986 aka bayyana shahararren mai horas war nan wato Sir Alex Perguson a matsayin mai horas da Manchester. Tun daga waccan rana yanayin wasa a Manchester ya sauya.
Sir Alex Perguson yazo da salon horas wa na yadda zai raini ɗanwasa tun daga ƙaramar ƙungiya kokuma ya sayo shi daga wata ƙungiyar tun bai zama wani ba sannan kuma ya mayar dashi wani harya addabi ƙungiyiyin ƙwallon ƙafa.
Sir Alex Perguson dai ya zamo mai sa’a a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United wanda tunda ƙungiyar take batayi mai horas wa kamarsa ba kuma har yanzu babu alamar za a sami wanda zai kafa tarihi kamarsa ba.
Mai horas war a iya shekarun daya kwashe tare da Manchester United ya lashe kofuna guda 36 inda daga ciki akwai gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila sannan kuma akwai gasar zakarun nahiyar turai guda 2. Sannan kuma akwai gasar F.A guda biyar, akwai gasar Super Cup guda 1, akwai gasar Community Shield guda 10, akwai gasar zakarun nahiyoyi guda 1 akwai gasar League Cup guda 4.