Za a iya cewa ƙungiyarƙwallon ƙafa ta Arsenal dake birnin London na ƙasar Ingila naci gaba da bin hanya mai tsauri kuma mai sarƙaƙiya a gasar League Cup da ake ci gaba da fafatawa a ƙasar Ingila, wasan da aka kammala zagaye na shida dana biyar da kuma zagaye na huɗu.
Gasar ta League Cup dai tuni aka fatattaki wasu daga cikin manayan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa, za a iya cewa sama da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa guda 60 ne suke fafata gasar amma a yanzu haka an kori guda 54 yayin da guda 8 ne kawai suka rage kuma sune zasu fafata wasan kusa dana kusa dana ƙarshe a gasar ta League Cup kuma wasannin na wannan kakar wasan sun banbanta dana sauran shekarun baya ganin yadda gumurzu yayi yawa a kusan kowanne wasa.
Arsenal dai itace ta zama kamar sha wuya a wannan kakar wasan duba da cewar tun wasan zagaye na biyar data fara bugawa to an bata hanya mai wahala, idan za a iya tunawa itadai Arsenal ta fafata wasanne da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leicester City wasan da Arsenal ta wanke Leicester daci 2 da nema kuma ta sami damar tsallakawa zagaye na huɗu a tsakiyar makon da ya gabata kenan.
Tsallakawar ta ke da wuya kawai aka basu ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool inda Arsenal ba tayi ƙasa a gwiwa ba wajen wanke Liverpool a daren jiya Alhamis, sannan yanzu kuma gashi ta tabbata cewar Arsenal zata fafata wasan kusa dana kusa dana ƙarshe da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City, za a iya cewa ta sake haɗawa wato yaro da mai gidansa ganin cewar Pep Guardiola da Mikel Arteta sunyi aiki tare a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City kafin ya dawo ya kama horas da ita kanta Arsenal.
Arsenal dai za a iya cewa an sami sauyi kuma sauyi mai kyau tun bayan zuwan mai horas wa Arteta duba da cewar tunda ya fara horas da ƙungiyar ta Arsenal sau 6 yayi rashin nasara, sannan ya lashe waaanni da yawa kuma ya lashewa Arsenal kofuna guda biyu a watan Ogusta ba ahekarar 2020, haka zalika zuwansa Arsenal ta sayi ‘yan wasa da dama sannan duk ‘yan wasan da suka bayyana sha’awarsu ta barin Arsenal suma sun janye maganar.
Amma hakan baya rasa nasaba da kyakykyawar fahimta da aka samu da hukumar gudanarwar ƙungiyar ta Arsenal da mai horas war da kuma shi daraktan sayen ‘yan wasa wato tshohon ɗan wasan na Arsenal kuma ɗan asalin ƙasar Brazil wato Edu, inda kusan duk wata kitimurmurar sayen ‘yan wasa shine sila a ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Arsenal a halin yanzu.
Ƙungiyoyi guda 8 da suka rage a gasar ta league Cup akwai Everton da Stoke City da Arsenal da Brentford da Tottenham da Manchester City da Newcastle da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United. Tun bayan kammala wasannin zagaye na huɗu aka fitar da jaddawalin yadda kowacce zata kara a abokiyarta a wasan kusa dana kusa dana ƙarshe.
Ga jerin yadda aka fitar da buga wasan zagaye na uku:
Arsenal zata fafata da Manchester City.
Stoke City zata kara da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham.
Brentford zata kara da Newcastle.
Ita kuwa Everton zatayi karon ƙaho da ƙaho da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United.
Arsenal dai tunda ta fara fafata wasa a wannan sabuwar kakar wasan ta sami nasara a kusan dukkanin wasannin ta, wasa ɗaya kawai tayi rashin nasara wato wasan da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta lallasata a gasar ajin Firimiyar ƙasar Ingila wato wasan mako na uku da suka fafata a makon daya gabata, sai dai za a iya cewa Arsenal zata fafata wasa a kwanannan kuma wasa mai zafi shima a gasar ta Firimiya inda zata kara da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United.