Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake kasar Ingila ta yi wuff da dan wasan gefe na kungiyar Benfica Nuno Tavares.
Cinikin dan wasan wanda ya fafata wasa da Arsenal a gadar Europa da ta gabata, ya faɗa ne kan euro miliyan takwas wanda kuma ya zama cinikinta na farko.
Tavares ya buga wasanni 25 wa Ƙungiyar Benfica a kakar da ta gabata kazalika ya buga wasa wa Ƙungiyar Portugal yan kasa da shekara 21.