Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta wanke ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United har gida a wasan mako na bakwai na gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila da suka fafata a wannan yammaci na ranar Lahadi daci 1 mai ban haushi wasan daya sake ɗaga darajar Arsenal.
Aubameyang ne ya tabbatarwa da Arsenal nasararta bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, za a iya cewa Arsenal ta kawo ƙarshen tsawon lokaci data kwashe bata iya samun nasara a filin wasa na Old Trafford inda ta fafata wasanni 13 ba tare da tayi nasara akan Manchester United ba.
Amma yau ta karya wannan lago, sakamakon wannan nasara da Arsenal tayi yasa ta baro matsayinta na 12 ta dawo matsayi na 8 da maki 12 daga cikin wasanni guda bakwai data fafata a gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila.
Arsenal dai bana tana yunƙurin buga wasa ne domin wakiltar ƙasar Ingila a gasar zakarun nahiyar turai wato a kakar wasa ta 2021 zuwa 2022. Arsenal dai tun bayan da mai horas wa Arsen Wenger ya ajiye aiki basa iya halartar gasar zakarun nahiyar turai.