Arsenal ta shirya sabunta kwangilar dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31, inda zai rika karbar £250,000 duk mako tare da karin alawus-alawus, a yunkurin da take yi na rarrashinsa ya ci gaba da zama kamar yadda jaridar Telegraph ta labarto.
Borussia Dortmund na son dauko dan wasan Werder Bremen dan kasar Kosovo Milot Rashica, mai shekara 20, a yayin da suke neman wanda zai maye gurbin dan wasan Ingila mai shekara 20 Jadon Sancho, wanda ake sa ran zai tafi Manchester United. (Telegraph)
Kocin Rangers Steven Gerrard, mai shekara 40, ya ki amincewa da tayin da aka yi masa na zama sabon kocin Bristol City.
Valencia na shirin zawarcin dan wasan Chelsea da Sufaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25, da kuma dan wasan Manchester City David Silva, mai shekara 34.