Arzikin mutane uku da suka fi kuɗi a Nijeriya ya ƙaru cikin shekara ɗaya, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana bayan fitar da jerin attajiran duniya na shekarar 2021.
Attajiran na Nijeriya sun haɗa da shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote da shugaban Glo da Conoil, Dr Mike Adenuga da kuma shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Isiyaka Rabiu.
Mujallar ta ce arzikinsu ya ƙaru zuwa dala biliyan 22.5 a cikin shekara ɗaya.
Jerin sunayen attajiran duniya da Forbes ta wallafa a ranar Talata ya ƙunshi attajiran Afrika 14 da suka fi kowa kuɗi a nahiyar.
Kuma har yanzu a cewar Forbes, shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ne attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka.
Forbes ta ce arzikin Dangote, ya ƙaru inda ya haura $11.5bn daga $ 8.3bn a shekarar 2020, wanda hakan ya sa ya zama mutum na 191 da ya fi kowa kuɗi a duniya.
Shugaban kamfanin Glo da Conoil, Dr Mike Adenuga, wanda shi ne na biyu mafi arziki a Nijeriya kuma na biyar a Afirka, shi ne na 440 a duniya inda arzikinsa ya ƙaru zuwa dala biliyan $6.1 daga dala biliyan $5.6 a bara.
Arzikin shugaban kamfanin BUA kuma Abdulsamad Rabiu, arzikinsa ya ƙaru zuwa dala biliyan $4.9 daga dala biliyan $2.9 a bara, kuma shi ne na 574 a jerin attajiran duniya kuma na shida a Afirka.