Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United dake Ƙasar Ingila ta nuna sha’awarta ta yon wuff da yar wasan Najeriya ta mata Asisat Oshola kamar yadda rahotanni suna ruwaito.
Kuma tun farko Kafafen yaɗa labaran kasar Spaniya da sanyin safiyar nan suka labarto cewa Ƙungiyar da Oshola ke fafata wasa a halin yanzu wato Barcelona ta nuna aniyar ta ta sakin yar wasan, duk da cewa babu wata yar wasa a Ƙungiyar da ta fi ta zura leda a bana.
Kwantiragin yar wasan zai kare ne da yankin na Catalonia a shekarar 2022 kuma har yanzu babu wani tabbaci ko Ƙungiyar za ta tsawaita mata shi don ci gaba zama a chan.
Jaridu da dama a Birtaniya sun habarto cewa a yanzu haka abin da United Kawai ke jira shine amincewar yar wasan gabannin ta kara tunkuda bukatar ta zuwa sama.
A yanzu haka Oshola na da kwallaye 15 a Gasar Primera Iberdrola kuma da ma tana da kwarewa ta fafata wasa a Kasar Ingila duba da cewa ta buga wasa wa Ƙungiyar mata ta Liverpool a 2015 da Arsenal a 2016