Kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa ta taka burki wa Arsenal kan dan wasan Norwich City Emiliano Buendia, inda ƙungiyoyin biyu suka cimma yarjejeniyar pam miliyan 30 kan dan wasan.
Wannan yarjejeniya tana nufin cewa yanzu Arsenal ta zama kuran baya kenan kan dan wasan.
Dan wasan dan kasar Argentina mai shekara 24 shine gwarzon dan wasan Norwich City na bana bayan da kungiyar ta lashe gasar Championship tare da dawowa gasar Firimiya na baɗi.
Kazalika akwai yiwuwar Villa ka iya yin kari kan wannan kuɗi, tare da yarjejeniyar cewa ko da yaushe dan wasan ka iya bankwana da ita idan bukatar hakan ta taso.
Tuni har an riga da yi wa dan wasan gwajin lafiya a kasar Argentina, inda yanzu abinda ya rage kawai shine tattara kayan ya koma birnin Landan.
Buendia ya lashe gasar Championship da Norwich har sau biyu, kana ya buga mata wasan Firimiya sau 36 wanda da ma a kakar 2019/2020 ne ta koma gasar gajiyayyu.