Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce ya yi maraba da sako ‘yan mata hudu da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a kauyen Kautikari da ke karamar hukumar Chibok a jihar Borno.
An sace ‘yan matan da aka sako ne a yankin Kautikari a farkon watan nan a karamar hukumar Chibok.
UNICEF a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin din nan ta bayyana jin dadi kan ‘yancin ‘yan matan tare da yin kira da a gaggauta sakin duk yaran da ke fama da rikici da ake tsare da su a fadin yankin.
Wakilin UNICEF a Najeriya, Peter Hawkins, ya ce “UNICEF ta yi matukar farin ciki ga ‘yan matan da aka sako da iyalansu.”
“Bayan abin da suka same su, labari ne mai daɗi cewa ‘yan matan sun dawo ga iyalai da abokansu, inda suke. Amma abin takaicin shi ne, yara da dama a arewa maso gabashin Najeriya sun ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa; wadanda rikicin makami ya shafa ba ruwansu da su. Wannan rashin hankali ne. Yara suna da ‘yancin samun muhalli mai aminci, lafiya, ilimi, da ‘yanci daga cin zarafi da azabtarwa – duk abin da ke cikin matsala lokacin da suke cikin zaman talala, ” Hawkins ya kara da cewa.
A shekarar 2014, garin Chibok ya dauki hankulan duniya bayan da aka sace ‘yan mata 276 a yankin.
A cewar UNICEF, kimanin 173 daga cikin ‘yan matan Chibok ne har yanzu ba a gansu ba. A watan Janairu, an kuma sace da yawa a Pemi, wata al’umma a karamar hukumar Chibok.
“Yara ba ganimar rikici ba ce. Dole ne a sako duk yaran da ake garkuwa da su cikin gaggawa kuma cikin aminci ga iyalansu,” in ji UNICEF.
Bisa kididdigar da UNICEF ta fitar, an sace akalla yara 1,450, akasari daga makarantunsu, a sassan tsakiya da arewa maso yammacin kasar tsakanin Disamba da Yuli 2021.