Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’ar nan a fadar gwamnati da ke Abuja, ya gana da shugabannni da mambobin iyayen jami’o’in tarayya, inda ya yi alkawarin ci gaba da tuntubar juna da masu ruwa da tsaki, domin kawo karshen yajin aikin da malaman jami’o’in suka dade suna yi, a karkashin kungiyar malaman jami’o’in (ASUU).
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Shugaban Ƙasar yace ba tare da komawa kan Dokar da tuni aka riga aka sanya ba ta babu aiki Babu Biyan Albashi, ya ƙara dacewa “zan tattauna tare da neman shawarwari, sannan zan sanar daku abinda na yanke.”
Iyayen Jami’o’in wanda Farfesa Nimi Briggs ya jagoranta, sun ce sun zo ne domin ganawa da shugaban kasa a matakai uku: “A matsayinsu na shugabanni kuma manyan jagorori, a matsayin ubannin kasa, kuma a matsayin shugabannin jami’o’i.”
Karanta kuma: Gwamnatin Tarayya Da ASUU: Kotu Da Dage Cigaba Da Zamata
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Farfesa Briggs ya kara da cewa, duk da matsalar da aka samu sama da watanni bakwai na ayyukan masana’antu, “makomar tsarin jami’o’i a kasar na da kyau,” inda ya ba da misali da jerin sunayen jami’ar Ibadan a cikin jami’o’i 1,000 na farko a duniya ci gaban da ke faruwa a karon farko.
Ya yabawa Gwamnatin Tarayya bisa rangwamen da ta yi wa malaman da suke yajin aiki, ciki har da tayin karin albashi da kashi 23.5% a fadin kasar, da kuma kashi 35 na Farfesoshi, duk da haka, ya nemi “kara yawan albashin, la’akari da yanayin tattalin arzikin kasar.”
Jagoran Iyayen jami’ar ya kuma bukaci a sake duba matsayin gwamnati na rashin aiki, rashin biyan albashi, tare da yin alkawarin cewa malamai za su gyara abin da ya baci da zarar an samu zaman lafiya, sannan a bude makarantu.
Karamin Ministan Ilimi, Goodluck Nana Opiah, ya ce duk wani rangwame da Gwamnatin Tarayya ta yi na ganin an kawo karshen yajin aikin jami’a’i, amma ASUU ta burus.
A wani labarin kuma: Dalibai Sun Ki Komawa Makaranta Saboda Tsoron ‘Yan Bindiga
Wasu daliban makarantun Firamare da Sakandare a jihar Kaduna, sun ki komawa makaranta domin gudanar da sabon zangon karatu saboda fargabar hare-haren ‘yan bindiga.
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana ranar 4 ga watan Satumba, na 2022, a matsayin ranar da za a bude dukkan makarantun jihar domin gudanar da sabon zango, sai dai makonni biyu da komawa makaranta, har yanzu wasu dalibai ba su koma aji ba sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda a cikin jihar.