Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hukumar gudanarwar jami’ar jihar Gombe (GSU) ta bayyana cewa ranar Litinin itace a matsayin ranar da za ta dawo da daliban jami’ar masu matakin karatu na 100.
A cikin wata takarda ta cikin gida mai dauke da sa hannun mataimakin magatakardar jami’ar Musa Sarki, wadda Jaridar Daily Trust ta samu a ranar Alhamis, an bukaci daukacin daliban jami’ar na aji 100 da su kai rahoto ga sashinsu na jami’ar a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Cafke Wani Mutumi Sanye Da Kayan Soji, Ɗauke Da Bindiga A Kano
“Sakamakon shawarwarin da aka yi tsakanin masu ruwa da tsaki a Jami’ar Jihar Gombe, an kuduri aniyar baiwa dalibai masu matakin karatu na 100 damar dawowa ranar Litinin 22 ga watan Agusta, 2022 domin kammala aikin rijistar,” in ji sanarwar.
Ya kara da cewa duk masu ruwa da tsaki sun amince cewa a ba wa daliban damar gudanar da kammala karatunsu na zangon farko na zangon karatu na 2021/2022.
Da aka tuntubi shugaban GSU reshen kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), Dr Sulaiman Salihu Jauro, ya ce zai yi magana da manema labarai ne kawai bayan taron kungiyar da za ta yi a ranar Juma’a.
A wani labarin kuma An kama wani da ake zargin wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba a jihar Kano sanye da kakin Sojoji da bindiga da harsashi.
An tattaro cewa wanda ake zargin ya kasance yana fakewa da sunan jami’in soji, mai suna M.A Ibrahim domin karbar kudi daga hannun mutanen da ke kan titin BUK mai farin jini a cikin babban birnin jihar.
Wani ganau da bai bayyana sunansa ba, ya ce wanda ake zargin yana zaune ne a unguwar Danbare da ke cikin BUK, kuma ya dade yana gaya wa mutane cewa shi kaftin ne a rundunar sojin Najeriya.
An bayyana cewa, an kama wanda ake zargin ne bayan da ya tabbatar da sakin budurwarsa da karfi, wadda jami’an Hisbah suka kama. An ce yayi harbi a saman iska a ofishin Hisbah kafin ya kubutar da ita.
Shaidun gani da idon sun ce, “Kun san jami’an Hisbah na zuwa ne su kamo mata masu zuwa shan kwaya da sauran abubuwan da ba su dace ba.”
“Haka suka kama budurwarsa suka kaita ofishinsu. Lokacin da ya isa ofishin Hisbah a nan Danbere, sai ya yi harbin a saman iska har sau uku ya tafi da ita.”
“Sai muka kai rahoto ga ‘yan sanda da sojoji a nan barikin Janguza. Da muka aika musu da hotunansa, sai suka gane cewa shi ba hafsan soja ba ne, sai suka ba da umarnin cewa duk lokacin da muka gan shi mu kira su. Da muka ga motarsa a ajiye a wani gidan mai, nan take muka kira su suka kama shi,” inji ganau.
Ya ce duk da cewa ba a kama wanda ake zargin a cikin motarsa ba, amma an samu bindiga da kakin sojoji a cikin motarsa.
Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar sojojin ta Kano kan lamarin bai yi nasara ba, domin lambar wayarsa bata shiga har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ya samu labarin lamarin amma ba a mika wanda ake zargin ga ‘yan sanda ba.
Ya yi alkawarin komawa ga wakilinmu da karin bayani.