ASUU: Malaman Kaduna sun Watsar da Maganar El-Rufai, Sun ƙi duba Jarrabawa
Ƙungiyar Malaman jami’o’in Najeriya ASUU reshen Jihar Kaduna (KASU) ta ki komawa karatu duk da barazanar da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi na korar su.
Hukumar kula da makarantar ta buƙaci Ɗaliban da su koma karatu domin jarrabawar su bayan barazanar da Gwamnan ya yi.
A ranar Litinin din da ta gabata ne aka ga wasu daga cikin daliban a darussa suna rubuta jarabawarsu ƙarƙashin kulawar Shugaban Jami’ar da sauran ma’aikata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga Sun Yi Garkuwa Da Majinyaciya A Zaria
Daily Trust ta tattaro cewa ‘ya’yan kungiyar ASUU sun ki shiga aikin sa ido inda suka yi ikirarin cewa yajin aikin na ci gaba da gudana don haka ba za su shiga jarrabawar ba.
Kungiyar a wani labari da ta fitar a karshen taronta na Jami’ar Kaduna da ta gudanar a ranar Litinin ta ce an samu kura-kurai a lokacin jarrabawar.
Shugaban Ƙungiyar ASUU -KASU reshen jihar, Kwamared Peter Adamu da Comrade Usman Abbas, Sakataren Ƙungiyar ne suka sanya wa kudurin sanya hannun.
Ƙudirorin sun kasance kamar haka “Ya kamata Ƙungiyar ta tattara duk wasu kura-kurai da rashin bin ka’ida da aka samu wajen gudanar da wasu ’yan jarrabawar da aka yi sannan kuma ta mikawa Hukumar Jami’ar Kasa.
“Mambobin ASUU-KASU ba su shiga domin gudanar da jarrabawa a jami’ar saboda yajin aikin da ake yi.
“Ana rubuta duk wani nau’i na cin zarafi na yajin aikin da mambobin kungiyar suke yi, kuma za a yi amfani da matakin ladabtarwa kamar yadda kundin tsarin mulkin kungiyar ya tanada a daidai lokacin da ya dace,” in ji shi.
A nasa martanin, Shugaban Jami’ar Farfesa Abdullahi Ashafa, ya ce, a bangaren hukumar, KASU- ASUU na goyon bayan Jami’o’in Tarayya ne kawai.
” A kan haka ne muka ga ya kamata mu kasance masu kishin kasa, dalibanmu sun shafe sama da watanni biyar suna gida ba tare da karatu b