Kungiyar Malaman Jami’oi a Nijeriya ta yi barazanar sake komawa yajin aikin da ta dakatar saboda abinda ta kira cin zarafin da ake yi wa mambobinta da kuma kin biyan su albashin su.
Kungiyar ta kuma zargi gwamnatin Najeriya da kin biyan albashin wasu malaman na ta na watanni 10 a wasu jami’oin dake cikin kasar.
Wata sanarwar da shugaban kungiyar Farfesa Ayo Akinwole ya rabawa manema labarai tace duk da dakatar da yajin aikin da suka yi a ranar 24 ga watan Disambar bara a karkashin yarjejeniyar cewar babu wanda za’a musgunawa saboda shiga yajin aikin, yanzu haka gwamnati taki biyan wasu daga cikin malaman da dama albashin su da ya kai na watanni 10.
Kungiyar tace halin da ake ciki na matsalar tattalin arziki ya shafi malaman wadanda tuni suka koma bakin aikin su kamar yadda suka yi alkawari, yayin da gwamnati taki kuma mika musu kudaden da ta cire daga albashin malaman domin aikin kungiyar.
Sanarwar ta bukaci Yan Najeriya da kar su ga laifin malaman idan sun koma yajin aikin domin kuwa gwamnatin kasar ce taki cika alkawarin da ta dauka.