Akalla dalibai 50 ne kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), daga jami’ar Nnamdi Azikiwe (NAU), reshen Awka, aka baiwa Naira 60,000 kowannensu domin tallafa musu.
Solacebase ta ruwaito cewa ma’aikatan koyarwa 50 na cibiyar da kuma mambobi 26 na kungiyar ASUU a jami’ar NAU da suka yi ritaya a tsakanin shekarar 2012 zuwa 2020, kungiyar ta kuma ba su lambar yabo.
An bayar da tallafin karatu da kyaututtuka ne a wani biki, wanda aka gudanar a sakatariyar kungiyar a ranar Laraba.
Shugaban kungiyar, Dokta Stephen Ufoaroh, ya bayyana cewa tallafin shine karo na biyu, kuma wani bangare ne na zamantakewar kungiyar ga daliban da iyayensu.
Ufoaroh ya ce daliban da suka ci gajiyar, wadan da galibinsu marasa galihu ne, an zabo su ne ta hanyar tsattsauran tsarin tantancewa da kwamitin daliban na ASUU.
Ya godewa ’yan kungiyar da suka bayar da gudunmuwarsu ga asusun duk da basussukan albashi da karin girma da aka gaza biyansu.
“Duk da cewa wasu ma’aikatan jami’ar UNIZIK na bin bashin albashi da karin girma, amma duk da haka ‘yan kungiyar ASUU a jami’ar NAU sun ga akwai bukatar su taimaka wajen rage radadin da daliban ke fuskanta.
“Wadannan ɗaliban suna ɗauke da radadin rashin kulawar masu mulki ga talakawan da ke shan wahala. Muna rokonku da ku cigaba da jajircewa wajen neman ilimi.
“ kungiyar ASUU ta kasa kuma ta bayar da tallafin karatu na N100,000 ga daliban da suka cancanta a jami’o’in gwamnati a Najeriya wanda dalibin UNIZIK ya ci gajiyar tallafin.
“Muna addu’a da fatan daliban za su yi amfani da wannan asusu don biyan kudaden makaranta, ta yadda za su ba wa iyayenku/masu daukar nauyin dan jin dadi na zaman karatu daya,” in ji shi.
Shima da yake nasa jawabin, shugaban ASUU na kasa Farfesa Emmanuel Osodoke, ya yabawa majalisar da shugabannin kungiyar da suka biyo bayan wannan karamci, inda ya yi addu’ar Allah ya sa kudin ya yi nisa wajen amfanar daliban.
Osodoke, wanda ya samu wakilcin Dokta Uzo Onyebinama, ya ce ASUU ta kasance kuma za ta ci gaba da kasancewa a sahun gaba wajen samar da ilimi kyauta a Najeriya.
A cewarsa, ASUU tana da yakinin cewa Najeriya na da karfin baiwa dukkan ‘yan kasarta ilimi kyauta idan har ana son siyasa,” inji shi.
Da yake mayar da martani a madadin wadanda suka yi ritaya, Farfesa Onyido ya bayyana kyautar a matsayin daya daga cikin mafi kyawu da ya samu daga mazabarsa.
Onyido ya ce yana godiya ga Allah da ya raya su domin shaida taron bayan gudanar da aikin nagari.
Ya ce wasu abokan aikinsu da suka shiga hidima tare da shi, ba su nan, yayin da wasu kuma ba su kai shekarun yin ritaya ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ma’aikacin mai ritaya ya godewa ASUU saboda tunawa da abokan aikina, inda ya kara da cewa: “A gare ni, wannan ita ce mafi kyawun kyaututtukan da na samu, daga mazaba ta.
“Littafi Mai Tsarki ya ce ba a san annabi a garinsu ba, amma hakan ya bambanta. Muna yi wa shugabanni addu’a kuma za mu ci gaba da ba su goyon baya ta fuskar tarbiyya da sauran su,” inji shi. (NAN)