Sabbin bayanai na ci gaba da fitowa kan dalilan da suka sanya kungiyar malaman Jami’o’i ta ki amincewa da tayin da gwamnatin tarayya ta yi mana.
A baya dai jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa ASUU ta zauna da gwamnatin tarayya tare da sauraren tayin, amma daga bisani kungiyar tayi fatali da shi.
Sai dai kuma kungiyar ba ta yi karin bayani ba a cikin kudurorin.
Jam’in Kungiyar shiyyar Fatakwal Stanley Ogoun, a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, ya bayyana cewa kungiyar ta lura da yunkurin gwamnatin tarayya na kara yawan albashin shehunan malaman jami’o’i da naira 60,000.
Yayin da sauran malaman za a kara musu albashi a cikin adadin albashin su yawan kuɗin da ya kai Naira 30,000.
Ogoun ya kuma lura cewa gwamnati ta yi alkawarin sakin kudaden farfado da jami’o’in naira biliyan 170 da za a saka a cikin kasafin kudin shekarar 2023.
“Yunkurin da Gwamnatin Tarayya ta yi a halin yanzu na yin watsi da bukatun mu kamar yadda muka gabatar mata, hakan na nuna cewa rashin kishin jami’o’in ne, kuma masu karatu a cikinta, kuma tayin kudin da tayi mana baza mu taba amincewa da shi ba.”
A don haka ƙungiyar ta yi kira ga Ministan Ilimi, Adamu Adamu da ya yi murabus.