Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi kira da a samar da kudirin doka da zai tsara yadda ‘ya’yan jami’an gwamnati ke shiga makarantun da ke wajen Najeriya da sunan karatu.
Shugaban Jami’ar Neja Delta Wilberforce Island Farfesa Kingdom Tombra ne ya bayyana haka a wata zanga-zangar hadin kai da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta shirya a jiya Talata a birnin Yenagoa.
JARIDAR DIMOKURAƊIYYA ta rawaito cewa kungiyar NLC ta fara zanga-zangar ne a fadin kasar domin nuna goyon bayanta ga kungiyar ASUU da sauran kungiyoyin da ke da alaka da harkar masana’antu a jami’o’in gwamnati a Najeriya.
DUBA WANNAN LABARIN: An tsaurara jami’an tsaro a harabar majalisar dokokin tarayya
“Idan aka yi haka, za a gina al’umma ta gari ta hanyar bunkasa manyan cibiyoyin ilimi da inganta kudade na tsarin jami’a a Najeriya.
“Wannan gwagwarmayar ba ta adawa da gwamnati ba ce, a’a ta bangaren ma’aikata da masu mulki ne kuma mun jajirce sosai “Idan masu hannu da shuni suka je jami’a ko cibiya daya, ba na jin za a sake yajin aikin.
“Idan sun yi makaranta a nan kuma ‘ya’yansu suna nan za su nuna cikakken goyon baya ga tsarin jami’a da kuma manyan makarantun Najeriya,” in ji shi.
Malaman jami’o’i mallakar gwamnati sun fara yajin aikin a fadin kasar a ranar 14 ga watan Fabrairu kan amincewa da tsarin bayar da tallafi na jami’o’in da sauran bukatu