Bangarorin kungiyar Malaman jami’a a Najeriya sun duba halin da ake ciki game da annobar COVID-19, sun ce bai dace a bude makarantu ba.
Sai da a ranar Lahadi Jaridar Punch ta fitar da dogon rahoto wanda ya nuna malaman jami’o’i da-dama basa goyon bayan Dalibai su koma fagen karatu a ranar 18 ga wata.
Kamar yadda ASUU tace ta shirya komawa aiki, amma gwamnati ba ta yi tanadin da ake bukata domin kare ma’aikata da dalibai daga kamuwa da COVID-19 ba.
Shugaban ASUU na jami’ar Obafemi Awolowo, Osun, Dr. Adeola Egbedokun yace dakunan kwana da na karatu sun saba sharudan yaki da annobar.
Haka zalika kungiyar ASUU ta jami’ar aikin gona ta tarayya da ke garin Abekoya, ta ce ba za ta iya tunkarar kalubalen annobar cutar Coronavirus ba.
Shugaban ASUU na jami’ar FUNAAB, Dr. Adebayo Oni ya yi hira da Punch, yace dakunansu a cike suke makil, kuma babu wuraren wanke hannuwa.
Malaman jami’an ATBU ta bakin shugaban ASUU na makarantar, Dr. Musa Babayo, yana kan wannan ra’ayi, yace hukumomi ba suyi wani tanadi ba.
Babayo yake cewa da aka tafi yajin aiki makarantu da gwamnati ba suyi wani kokarin ganin yadda za a tunkari annobar a dakunan aji da karatu ba.
ASUU ta reshen jami’ar UNIJOS, tana tsoron halin da ake ciki. Shugaban kungiyar, Dr. Lazarus Maigoro yace babu shakka cutar COVID-19 ta sake barkewa.
Shugabannin ASUU na jami’o’in Calabar da Fatakwal, Dr John Edor da Dr Austen Sado, basu goyon bayan a jefa malamai cikin hadari da komawa bakin karatu.
Jami’o’in Bayero da ke Kano, da UNIBEN da ke jihar Edo, da kuma jami’ar tarayya ta Ilorin duk sun yi alkawarin zasu koma bakin aiki a cikin watan Janairu.
Ita dai gwamnatin tarayya ta bakin hukumar NUC ta umurci jami’o’in kasar su fara shirin komawa aiki.