Kungiyar malaman jami’o’i ta dage cewa mambobinta ba za su koma bakin aiki ba duk da biyan mafi karancin albashin ma’aikata da gwamnatin tarayya ta yi musu.
Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata Sanarwa da ƙungiyar reshen Jami’ar Legas mai take, ‘Biyan bashin mafi ƙarancin albashi’.
Shugaban kungiyar ASUU reshen UNILAG, Dele Ashiru, ya tabbatar da sahihancin kudurin nasu a wata Sanarwa da suka fitar a yau Asabar mai dauke da sa hannunsa.
Ashiru ya bayyana biyan basussukan da aka dade ba a biya ba, yana mai cewa ba a biya manyan bukatun ASUU ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Shugabancin Reshen mu ya cika da kiraye-kirayen da suka shafi biyan basukan da aka dade a baya na gyara mafi karancin albashin ma’aikata.
“Muna tunatar da mambobinmu cewa wannan baya daya daga cikin muhimman bukatun da suka sanya mu fara gudanarwa da yajin aikin.
Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta fara biyan mafi karancin albashin ma’aikata, wanda malaman ke bin gwamnatin, a karkashin kungiyar malaman jami’o’i.