Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa ASUU a ranar Talata ta ce ba ta da wani shiri na dakatar da yajin aikin da ta ke yi sai dai kawo karshensa na dindindin.
Sai dai ya ce irin janyewar na iya faruwa ne kawai idan an biya dukkan bukatun.
Shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja.
“Muna son kawo karshen yajin aikin. Ba mu dakatar da yajin aikin ba. Za ku iya kawo karshen yajin aikin ne kawai idan an biya dukkan bukatun mu,” inji shi yayin da yake martani ga Gwamnatin Tarayya.
Yayin da yake yaba kokarin wasu masu ruwa da tsaki kan yajin aikin, Osodeke, ya ce “ba a gama ba har sai an gama biyan bukatun kungiyar!”
A wani rahoto da kafafen yada labarai ke yadawa cewa Gwamnatin Tarayya na shirin kara albashin ‘yan kungiyar ASUU da kashi 100, Osodeke ya ce, “Ba mu da masaniya kan wata sabuwar yarjejeniya. Idan gwamnati na son tattaunawa da mu, sun san hanyar da ta dace.”
Tun da farko a wata hira da jaridar The PUNCH, Osodeke ya ce har yanzu kungiyar ba ta samu wani kira ko gayyata daga gwamnati ba tun bayan ganawar karshe da Farfesa Nimi Briggs a ranar 16 ga watan Yuni shekarar 2022.
Wannan na zuwa yayin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, ya umurci ministan ilimi, Adamu Adamu, da ya kawo karshen yajin aikin watanni biyar da ASUU da wasu kungiyoyin kwadagon jami’o’i uku su ke yi, cikin makonni biyu.
Buhari ya bayar da wa’adin ne bayan da ma’aikatu da hukumomi da ma’aikatun gwamnati da ke ci gaba da tattaunawa kan yadda za a sasanta tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago sun yi masa bayani.
Bayan jawabin ne daga MDAs da dangogin su, shugaban ya umurci ministan ilimi da ya kawo karshen duk wata takun saka tsakaninsa da ASUU a cikin makonni biyu tare da kawo masa rahoto matakin da ya dauka.