Reshen kungiyar malaman jami’o’i ASUU ya soki nadin Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Dr. Isa Ali Pantami, a matsayin Farfesa a fannin tsaro ta yanar gizo wanda majalisar gudanarwa ta Jami’ar Fasaha ta Tarayya ta Owerri (FUTO) tayi ikirarin bashi.
Kungiyar ta ce akwai hanyoyi da dama wadanda ya kamata ace sun bi wajen bashi wannan mukami amma kuma suka gaza hakan.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an tafka cece-kuce a kan nadin da jami’ar FUTO ta yi wa Ministan a matsayin Farfesa.
Shugaban jami’ar ATBU, Farfesa Mohammad Abdulaziz, a wata wasika da ya rubuta a madadin hukumar gudanarwa, ma’aikata, da daliban cibiyar, ya taya Pantami murna kan nadin da aka yi masa amma kungiyar ASUU ta ware kanta daga wasikar taya murnar.
Da yake jawabi ga manema labarai a Sakatariyar da ke Bauchi, a yau Alhamis, shugaban ASUU na Bauchi, Dakta Ibrahim Inuwa, ya ce: “Nadin wani a matsayin Farfesa ya bi wasu ka’idoji, har ma mun gamsu da cewa ana bin wadannan ka’idoji sosai amma abin ya ci tura. har yanzu abin tambaya ne. Amma idan aka tabbatar ba tare da wata shakka ba, ba mu da wani zaɓi sai dai mu yarda da shi amma a yanzu, ba mu da tabbas.”