Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ta maka gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki a gaban kotu bisa dakatar da duk wasu ayyukan kungiyar a manyan makarantun jihar.
A cikin karar da ta shigar a gaban kotun masana’antu ta kasa da ke garin Benin kan jami’ar Ambrose Alli da Gwamnatin jihar ta ce, ta dakatar da ayyukan kungiyar ASUU a jami’ar, ASUU ta ce hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Sauran wadanda kungiyar ta maka agaban kotun sun hada da: gwamnatin jihar Edo, babban lauya jihar, da kuma kwamishinan shari’a na jihar.
Sai dai harkawo hada wannan rahoton, Kotun ta ba sanya ranar da zata fara sauraron karar ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Edo ta bakin sakataren gwamnatin jihar, Osarodion Ogie, ta sanar da dakatar da ayyukan kungiyar a cibiyoyin gwamnati, biyo bayan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in ta kasa (ASUU) ta shiga.