Daliban jami’a zasu cigaba da zaman gida tsawon wata 3 nan gaba a Najeriya, bayan da Kungiyar Malaman Jami’an ta sanar da tsawaita yajin aikin da take yi.
Wannan matsaya da kungiyar ta dauka ya faru ne yayin zaman majalisar kolinta, daren Jiya a Abuja, bayan gaza cimma matsaya a tsakaninta da gwamnatin tarayya.
ASUU tace zata cigaba da yajin aikin daga yau litinin 9 ga watan da muke ciki har zuwa watan Agusta.
Shugaban ASUU Emmanuel Asodeke ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ASUU ta fitar ga manema labarai a yau Litinin.
ASUU tace ta dauki wannan mataki bayan kwamitinta na zartarwa yayi taron gaggawa a Abuja.
Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Dalibai tuni suka fara kokawa kan zaman gidan da suke sakamakon yakin aikin malaman nasu.
Yayin da ita kuma gwamnatin tarayya ta gaza cika bukatun da kungiyar ke naman a cika mata.