ASUU ta yi zazzafan martani kan kudirin iyaye na biyan N10,000
Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta yi watsi da shawarar da kungiyar iyaye da malamai ta kasa ta yi na biyan kungiyar akalla N10,000 ga kowane iyaye a kowane bangare na ilimi a kokarin kawo karshen yajin aiki
KARANTA WANNAN LABARIN: Da dumi-dumi: Tsohon Shugaban Shirin Sulhu na Neja Delta, Dokubo ya rasu
DAILY POST ta tuna cewa Jami’in Hulda da Jama’a na NAPTAN, Dokta Ademola Ekundayo, a wata hira da aka yi da shi a baya-bayan nan, ya ce sun dauki wannan matakin ne don taimakawa Gwamnatin Tarayya ta biya bukatun ASUU.
Da yake mayar da martani kan shawarar, Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke yayin da yake bayyana a gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis ya yi watsi da tayin, inda ya bukaci kungiyar da ta kara matsa lamba kan FG.
Ya ce, “Ina ganin abin da ya kamata wannan kungiyar ta yi shi ne ta gaya wa gwamnati ta yi aikinta. Kamata ya yi su matsa wa gwamnati ta yi amfani da kudin ‘yan Najeriya wajen samar da ilimi kamar yadda ake yi a wasu kasashe.
“Ba za mu iya kiran kanmu ‘yan Afirka ba kuma mu ne mafi munin ilimi. Za ka ga dalibai daga Najeriya suna zuwa Ghana, Jamhuriyar Benin, Togo, da sauran kananan kasashe don yin karatu amma ba wani daga wadannan kasashen da ke zuwa Najeriya karatu.
“Don haka ya kamata su kara matsin lamba daga ASUU na ganin gwamnati ta ba ilimi fifiko. Hakan ya fi N10,000 muhimmanci