Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen Jami’ar Usmanu Danfidiyo Sokoto ta zargi Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Mista Chris Ngige da rashin fadawa ‘yan Najeriya gaskiyar halin da ASUU ke ciki kan rikicinsu da Gwamnatin Tarayya.
Kungiyar a wani taron manema labarai da ta gudanar a jiya Lahadi, a sakatariyar kungiyar ‘yan jaridu ta kasa dake Zuru kan titin zuwa Sokoto, ta bayyana ministan kwadago Ngige a matsayin wani cikas a tattaunawar da kungiyar ta ASUU da gwamnatin tarayya ke yi.
Wadda kuma tattaunawa ce kan yadda za a kawo karshen yajin aikin da ASUU ta dade tana yi.
Shugaban kungiyar Mista MN Almustapha a jawabinsa ga manema labarai ya ce Minista Ngige ya yi zargin cewa ASUU reshen Sakkwato ta yaye daliban likitanci a lokacin da suke yajin aikin, inda ya kara da cewa ASUU reshen jami’ar Usmanu Danfidiyo ba ta yaye ko wane dalibi tun da aka fara yajin aikin.
Tun daga watan Fabrairu Kungiyar ta kalubalanci Ministan Kwadago da ya gabatar da duk wata hujja ta gaskiya da za ta goyi bayan ikirarin nasa da suka yi wa lakabi da karya.
Ya ce babu wata wasika da Shugaban Jami’ar Usman Danfodiyo Sokoto ya rubuta, ko daya daga cikin wakilansa ko wani jami’in kungiyar da ke nuna cewa malaman Likitan ba sa yajin aiki a UDUS.
A cewar ASUU, ministan na kwadago ya yi nasarar yaudarar masu ruwa da tsaki a fafutukar cewa ba za a iya warware matsalar da ke tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya ba.