Shugaban kungiyar malaman jami’o’I ta kasa {ASUU} Emmanuel Osodeke, yayi Karin haske kan yadda kungiyar su ta yi watsi da kudurin gwamnatin tarayya, na kokarin kara yawan kudin makarantar da daliban jami’o’i a Najeriya suke biya, zuwa naira miliyan daya.
Osodeke ya ce hakan ta faru ne yayin wani taron tattaunawa da nufin fahimtar da suka gudanar da gwamnatin a yan kwanakin da suka gabata, kuma anan ne ta bujuro musu da wannan bukatar, wadda kuma nan take suka yi watsi da ita.
Shugaban ASUU ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga mahalarta wani taron wuni guda, da aka shirya da nufin tattaunawa kan batutuwan da suka shafi kasa, wanda kuma reshen kungiyar dake jihar Bauchi suka shirya.
“gwamnati ta bujiro mana da cewa ya kamata dalibai su dinga biyan naira miliyan daya duk shekara, amma bamu amince da hakan ba, duba da yanayin da ake ciki wanda a hakan ma ba kowane yake samun damar karatun ba.’’ inji Emmanuel Osodeke